Gwamnatin tarayya ta bukaci tsagerun yankin Niger Delta da kada su cigaba da fasa bututun mai


Gwamnatin tarayya tayi kira ga yan kungiyar ta adda dake yankin Niger Delta wacce akafi sani da NDF (Niger Delta Avengers)  a turance da suka rika fasa bututun mai a shekarar da ta wuce kan su kara hakuri su kuma kwantar da hankulansu.

Da yakewa yan jaridar dake dauko rahoto daga fadar shugaban kasa jawabi,ranar Litinin bayan ya ganawa gana da shugaban kasa Muhammad Buhari, Ministan Harkokin yankin Niger Delta,Usani Uguru Usani ya ce gwamnati bata saba alkawarin da tayi ba kamar yadda kungiyar tayi ikirari.

Kungiyar a ranar Juma’a ta zargi gwamnatin tarayya da gazawa wajen cika alkawarin da tayi inda tayi barazanar ci gaba da fasa kadarorin mai.

Ministan yace kari akan umarnin da mataimakin shugaban kasa,Yemi Osinbajo ya bayar cewa a ware ₦5 biliyan domin fara aikin jami’ar Okerekoko kana ya ce shirin yin kananan matatun man fetur shi ma yana nan ba a dakatar dashi ba.

Ministan ya lura cewa babu wata kungiya da ta daga yankin dake san tattaunawa da Gwamnatin tarayya amma aka hanata.
Ministan yace gwamnati na duba wasu hanyoyin samun kuɗi domin kammala titin da ake kira titin  East West wanda na da matuƙar muhimmanci ga mutanen yankin baki daya.

You may also like