Gwamnatin tarayya ta daukaka kara kan hukuncin umurnin sake shugaban ‘yan kungiyar Shi’a ta harkar musulunci Ibrahim Elzakzaky da matar sa Zeenatu da alkalin babbar kotun taraiya Gebriel Kolawole ya yanke.
Ma’aikatar tsaro, Jami’an tsaron farin kaya DSS da ma’aikatar shari’a sun kalubalanci hukuncin babbar kotun a kotun daukaka kara da nuna cewa alkalin ya gwama kararraki a waje daya ya yanke hukunci cikin kuskure.
Rushe gidan Elzakzaky ya auku ne a jihar Kaduna,don haka wannan wata shari’a ce da babbar kotun ba ta hurumin sauraro don haka umurnin gina gida ga Elzakzaky da ba wa matar sa diyyar Naira miliyan 50 wassu shari’u ne na daban.
Sabuwar karar ta shafi caji 7 ga shugaban kungiyar ‘yan Shi’an da ke tsare don Disambar 2015 bayan arangamar sojoji da ‘yan Shi’a a Zaria da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan Shi’an da dama inda wani soja daya ya rasa ran sa.
Da alamun wannan shari’ar za ta dau lokaci kuma za ta iya kai wa har ga kotun koli.
Daliban kungiyar Shi’a kan yi zanga-zanga a Abuja don neman sako jagoran na su da hakan har ya kai su ga kai korafi ga hukumar kare hakkin ‘yan adam.
A zanga-zangar su ta karshe, daliban ‘yan Shi’an sun gamu da fushin ‘yan sanda da su ka jefa musu barkonon tsohuwa.