Gwamnatin Tarayya Ta Fara Aiwatar Da Shirin Ciyar Da Daliban Firamare Gwamnatin Shugaba Muhammad Buhari ta saki Naira milyan 375 ga jihohi biyar don fara aiwatar da shirin ciyar da daliban makarantun Firamare 700,000.
Kakakin Mukaddashin Shugaban Kasa, Laolu Akande ya ce jihohin da suka fara cin gajiyar shirin sun hada da; Anambra, Ogun, Oyo, Osun da Ebonyi inda ya kara da cewa a cikin wannan mako za a kara Sakin sama da Naira milyan 200 ga jihohin Zamfara da Enugu.

You may also like