Gwamnatin Tarayya ta Fara Biyan N5000 Duk Wata ga Marasa Galihu


 

Gwamnatin Tarayya ta fara cika alkawarinta na tallafawa marasa galihu da Naira 5000 duk wata daga sansanin ‘yan gudun hijira na Borno.

A karkashin shirin, wanda ya na daya daga cikin alkawarurrukan da shugaban kasa Buhari ya dauka a lokacin yakin neman zabe, marasa galihu guda miliyan daya za su na samun tallafin a kowanne wata.

A wata sanarwa da ya fitar, Laolu Akande, Mai bada shawara na musammam ga mataimakin shugaban kasa farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa za’a biya wadanda suka ci moriyar shirin ne kai tsaye ta hanyar da ta fi sauki.

Ya kara da cewa gwamnatin na aiki tare da gidauniyar Bill gates da majalisar dinkin duniya domin a fitar da hanyar biya da ta fi inganci.

Ya ce gaba daya an kiyasce cewa kimanin Naira biliyan 60 za’a biya ga marasa galihun.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like