Gwamnatin Tarayya Ta Fito Da Sabuwar Ka’idar Bayar Da Lambar MotaMinistan Kudi, Misis Kemi Adeosun ta bayyana cewa daga watan Maris na shekarar 2017, duk motar da ba ta da cikakken takardun shigowa da ita daga waje, ba za a yi mata lamba ba.
Ministar ta nuna cewa bin matakin ya zama dole don dakile ayyukan ‘yan fasa gwabri da ke shigo da Motoci ta barayin hanyoyi da kuma bunkasa yawan kudaden shiga da gwamnati ke samu. Haka nan kuma, Shugaban Kwastan na kasa, Kanal Hamid Ali ( Mai Ritaya) ya tabbatar da cewa kashi 70 cikin 100 na motocin da ake amfani da su a Nijeriya ba su da Cikakkun takardun shigowa da su daga waje.

You may also like