Gwamnatin Nijeriya ta hannun ministan labaru Lai Muhammed ta gaiyaci ‘yan gwagwarmayar ceto matan Chibok “BBOG” da su zabi mutum 3 da za a sanya su a tawagar rundunar sojan Nijeriya zuwa Sambisa don duba yunkurin da sojoji su ke yi na ceto sauran matan 195.
Tawagar a jirgin sojoji za ta tashi daga Abuja zuwa Yola a gobe Litinin da safe.
A nata martanin, kungiyar “BBOG” ta nuna farin cikin gaiyatar sai dai ta ce ta na son a yi wani taron shirin tafiya tukun kafin daukar mataki na gaba.
Kungiyar ta ruiwaito kamfanin dillancin labarun Nijeriya na sukar kungiyar ta ‘BBOG” da tallafawa tashin-tsahina a fakaice.
Don haka samun wannan gaiyata da ta shafi sojoji bayan wannan sukar ta sanya BBOG shiga kokonto.