Gwamnatin Tarayya Ta Gaza Matuka – Dr. Bugaje


An bayyana cewar ko shakka babu Gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugabanta Buhari ta gaza kuma ta fadi warwas waje kare bukatun Jama’ar Nijeriya musanman Jama’ar Arewa wadanda suka fito kwai da kwarkwata suka zabe ta, inda maimakon jama’a su ga canjin da ake yi musu romon baka a kai, sai ya zamana anyi musu mummunar sakayya ta fuskar fuskantar tsananin kashe kashe da bala’in yunwa da talauci, wanda tarihin kasar nan bai taba shaida irin shi ba.

Bayanin haka ya fito ne daga bakin sanannen Malamin Jami’ar nan Dakta Usman Bugaje, lokacin da yake zantawa da manema labarai jim kadan bayan kammala Laccar Azumin Watan Ramadan, da Kungiyar Jama’atu Nasril Islam karkashin jagorancin mai alfarma Sarkin Musulmi Dr Sa’adu Abubakar ta shirya, wanda ya gudana a Hedikwatar Kungiyar dake Kaduna.

Dakta Bugaje ya cigaba da cewar, a yadda Jama’ar Nijeriya suka shaida shine, an shiga cikin wani mawuyacin hali a kasar nan a lokacin Gwamnatin baya ta PDP, dalilin da ya sanya jama’a kuka da neman canji kenan, wannan ya sa jama’a gaba daya suka mika yadda da amincewar su ga Buhari, amma abin mamaki da takaici sai gashi Buhari ya gaza kai banten shi, ya watsawa Talakawan da suka zabe shi kasa a idanuwa, Al’umma suka shiga rudani da talabebiya, kuma ina tabbatar muku wallahi idan kasar nan ta cigaba da tafiya akan wannan tsari na shugabancin Allah kadai ya san makomar kasar anan gaba, domin mun kama hanyar zamowa tamkar kasar Laberiya ko Somaliya inji shi.

Masanin harkokin siyasar ya kara da cewar, abin takaici ne matuka yadda Jihohin Arewacin kasar nan suka zamo tamkar Mayanka ta yanka Mutane, Jihohi irin su Zamfara, Kaduna, Filato da Binuwai da Taraba da jihar Adamawa suka zamo wani sansani na kisan jama’a, a daidai lokacin da Gwamnatin Buhari ke ikirarin wai tayi nasara akan harkokin tsaro, lallai wannan abin bakin ciki ne matuka.

Dakta Usman Bugaje ya kuma yi kira ga dukkanin ‘Yan Nijeriya da cewar, suyi amfani da damar da ke hannun su wajen zaben wadanda suka cancanta ba wai biyewa Jam’iyyar wani ba, domin zabo wadanda suka cancanta sannan wadanda za su kai su ga tudun mun tsira, a babban zabe na kasa da ke tafe a shekarar 2019.

You may also like