Gwamnatin tarayya ta hana samar da maganin tari mai dauke da sinadarin Codeine


Gwamnatin tarayya ta hana samarwa ko kuma shigowa da magani tari dake dauke da sinadarin Codeine.

Isaac Adewale, ministan lafiya shine ya bawa hukumar tabbatar da ingancin abinci da kuma magunguna ta kasa NAFDAC, wannan umarni a ranar Talata bayan da kafar yada labarai ta BBC ta nuna wani rahoto kan binciken da ta gudanar akan shan maganin tarin a wasu jihohin kasarnan.

Rahoton na BBC ya nuna yadda shan maganin tarin domin bugarwa ya zama ruwan dare a tsakanin matasa.

Adewale ya ce hakan ya zama dole duba da yadda ake yawan shan maganin ba bisa ka’ida ba.

Rahoton ya kuma nuna yadda ake hada baki da wasu ma’aikatan kamfanonin samar da magani domin a sayar da maganin a kasuwannin bayan Fagge.

You may also like