Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi ta kwaso yan Najeriya 480 da suka makale a ƙasar Libya.
Kwaso yan ragowar Najeriya sama 4511 biyo baya bada jimawa. Dukkanin wadanda aka kwaso an ajiye su wani sansani dake Fatakwal na wucin gadi kafin a mayar dasu jihohin da suka fito.
Cikin farin ciki da annashuwa waɗanda suka dawo sun samu rakiyar Mustapha Maihaja shugaban Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Ƙasa NEMA, Abike Dabiri-Erewa mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin ƙasashen waje da kuma wakilin mai bawa shugaban ƙasa shawara kan harkar tsaro.
Tawagar ministan harkokin wajen Najeriya, Geoffrey Onyeama itace ta tattauna da gwamnatin kasar Libiya kan dawo da yan Najeriyar zuwa gida.
Mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Fatakwal da misalin karfe 5:05 na yamma inda suka samu tarba daga Onyeama da kuma sauran yan tawagar.
Da yakewa mutanen jawabi Onyeama yace:” Amadadin shugaban ƙasa ina yi muku murnar dawowa gida. Mai girma shugaban kasa da sauran yan Najeriya sun damu matuka da halin da kuke ciki shiyasa suka tura wakilai. Shugaban kasa yayi amfani da dukkanin wani karfin iko da muke dashi dan ganin an dawo daku gida.