Gwamnatin Tarayya Ta Maka Babban Mai Shari’a Na Babban Kotun Tarayya A Kotu 



 A yau Talata ne gwamnatin tarayya ta maka babban mai shari’a na babban kotun tarayya, Mai Shari’a Adeniyi Ademola a babban kotun tarayya dake Abuja.
Mista Ademola dai yana daga cikin alkalan da jami’an DSS suka kai samame gidajen su a ranar 8 ga watan Oktoba na wannan shekarar bisa zargin su da rashawa, inda ake zarginsa da karbar makudan kudade a matsayin na goro.
Mista Ademola da matarsa, Olubowale ana tuhumarsu da laifuka 15.

You may also like