Gwamnatin tarayya ta miƙa wa Kamaru shugabannin ƙungiyar ƴan awaren ƙasar


Julius Tabe, shugaban ƙungiyar ƴan awaren ƙasar Kamaru

Gwamnatin tarayya ta tasa ƙeyar Shugabannin ƙungiyar ƴan awaren ƙasar Kamaru dake fafutukar neman ɓallewa daga ƙasar waɗanda aka kama a wani Otal dake Abuja lokacin da suke tsaka da gudanar da taro.

Cikin waɗanda aka tasa ƙeyar ta su sun haɗa da Julius Tabe, Nfor Nfor, Fidelis Che, Henry Kimeng, Cornelius Kwanga, Tasang Wilfred, Eyambe Elias, Ojong Okongwo da kuma Nalowa Bih.

A wata sanarwa da ministan sadarwar ƙasar Issa Tchiroma Bakary ya tabbatar da cewa an mayar da shugabannin kungiyar yan awaren zuwa gida inda yaci alwashin cewa zasu fuskanci hukunci dai-dai da laifin da suka aikata.

“Rukunin ƴan ta’adda 47 cikinsu akwai Mista Ayuk Tabe,sun shafe wasu a wanni a hannun jami’an ƙasar Kamaru kafin daga bisani su fuskanci shari’a dai-dai da laifin da suka aikata,”sanarwar tace.

Bakary  ya yaba da haɗin kan da aka samu tsakanin Najeriya da Kamaru inda ya ce ƙasashen biyu baza su yarda a yi amfani da ɗayansu ba wajen yin abin da zai kawo rashin zaman lafiya a ɗaya daga cikinsu.

Yankin yammacin ƙasar ta Kamaru dake magana da harshen Ingilishi ya ɗade yana fafutukar neman ɓallewa daga ƙasar bisa abinda suka kira nuna wariya da ake nuna musu.

Fafatukar tasu ta ƙara ƙamari ne bayan da lauyoyi da malaman makaranta a yankin suka shiga wani yajin aiki da kuma zanga-zanga.

Sai dai gwamnati tayi amfani da ƙarfi wajen murkushe zanga-zangar ta hanyar katse intanet a yankin da kuma amfani da jami’an tsaro wajen kama mutane babu gaira babu dalili.  

You may also like