Gwamnatin shugaban Ƙasa Muhammad Buhari ta saki kuɗi har Naira biliyan 54 don biyan kudin fansho da ba abiya na shekarun 2014,2015 da kuma 2016.
Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar kuɗi ta ƙasa Salisu Na’inna Dambatta ya bayyana haka a jiya laraba inda yace tuni aka saki naira biliyan N45.5 ga hukumar fansho ta kasa.
Yace kuɗin da aka saka za a biya ma’aikatan da sukayi ritaya karkashin sabon tsarin biyan kuɗin fansho na ƙasa,da kuma waɗanda ba abiya ba.
Ɗambatta ya jiyo daga bakin ministar kudi Kemi Adeosun na cewa naira biliyan 12.5 biyan bashine na watan Janairu,faburairu da kuma Maris.
“Duk da yawan bukatu da ake dasu kan kudade da gwamnati take dasu shuga,Shugaban kasa muhammadu Buhari ya samu matuka da halin da ma’aikata da Yan fansho suke ciki “tace