Gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya karbi sababbin motocin kashe gobara guda biyu da kowacce kudinta ya kai dalar Amurka $250,000 kwatankwacin naira miliyan ₦90,000,000. da kuma wasu sababbin tankokin ruwa guda biyu.
Motocin tallafin ne daga gwamnatin tarayya ta ƙarƙashin ma’aikatar cikin gida.
Idan za’a iya tunawa gwamna Abdullahi Umar Ganduje,ya roki shugaban kasa Muhammad Buhari lokacin da ya kai ziyara aiki jihar kan ya taimaka wa jihar da kayan kashe gobara duba da yadda gobara tayi barna a wasu kasuwanni 7 dake jihar inda hakan ya jawo asarar dukiya ta biliyoyin naira.
Sakamakon wancan rokon da gwamnan ya yi a yau ya karbi wadannan motoci a madadin gwamnatin jihar Kano.