Rahotanni na nuna cewa gwamnatin Nijeriya ta yi alwashin sayar da wasu daga cikin matatun manta idan har basu fara kawo riba ba yadda ya kamata. Wani sabon kudiri a bangaren harkar mai da iskar gas na kasar shi ya tanadar da hakan.
Sai dai kudirin ya bayyana cewa ba za a sayarda matatun ba har sai an ba su tallafi da kuma lokaci na ganin ko za su farfado.
Wannan mataki ya biyo bayan yunkurin gwamnatin na rage rawar da ta ke takawa a masana’antun man fetur da iskar gas a kasar, domin inganta bangaren.
Dama dai Nijeriya na da matatun mai guda hudu ne kawai wadanda ba sa amfaninsu yadda ya kamata, duk da haka dai suna iya samar da gangunan mai miliyan 2 a kullum, yayin da ake shigo da sauran daga kasashen waje.
Sabon kudirin dai ya samar da hanyoyi daban daban da za’a inganta bangaren man fetur da iskar gas a kasar, a ciki har da samar da hukumar saka ido kan albarkatun mai wacce za a kira Petroleum Regulatory Commission.