Gwamnatin tarayya a ranar Lahadi ta ce ƴan matan sakandaren Dapchi 111 sune ya zuwa yanzu ba a iya gani ba bayan harin da ƙungiyar Boko Haram ta kai makarantar.
Lai Muhammad, ministan yaɗa labarai shine ya tabbatar da haka a Damaturu bayan wata ganawar sirri tsakanin jakadun gwamanatin tarayya,gwamanatin jihar Yobe, jami’an tsaro, shugabannin al’umma da kuma iyayen ƴan matan da suka ɓata.
“Ganawa ce ta masu ruwa da tsaki domin samun cikakken bayani kuma cikin ɗalibai 906 da aka tabbatar suna makarantar a wannan rana, ɗalibai 110 ne ba a san ina suka shiga ba,”ya ce.
Ministan ya ce an cimma abubuwa da dama a taron ciki har da tura jami’an ƴan sanda da na NSCDC zuwa dukkanin makarantun dake jihar.
Ya ce hukumomin tsaro suna aiki kafada da kafada don ganin cewa an samu nasarar ceto ƴan matan.