Ministan tama da karafa, Dakta Fayemi Kayode ne ya tabbatar da hakan, inda ya kara da cewa tattaunawa ta yi nisa tsakanin Gwamnatin tarayya da kamfanin Global Steel Holdings Limited, game da kamfanin.
Kamfanin karafan wanda aka kafa tun a 1983 shine mafi girma a Nahiyar Afrika amma Gwamnatocin baya suka yi watsi da shi duk da makudan kudaden da kasar nan ta kashe wajen gina shi.
Minstan ya ce sun duba lafiyar na’urorinsa da kuma matsalolin da suka hana kamfanin aiki domin sanin tushen matsalolin da nufin magancesu.