Gwamnatin tarayya tayi watsi da sharuɗan da ƙasar Amurika ta gindaya kafin sayar mata da jiragen yaƙi



Gwamnatin tarayya ta ce baza ta yarda da sharuɗan da ƙasar Amurika ta gindaya ba kan sayarwa da ƙasar na wasu jiragen yaƙi na zunzurutun kuɗi dala miliyan $494.

Mansur Dan-Ali, ministan tsaro shine ya bayyana haka ranar Alhamis lokacin da yake wa manema labarai jawabi a fadar shugaban ƙasa kan zaman taron majalisar tsaron ƙasa.

Wani bangare na sharuɗan sayar da jiragen 12 sanfurin A-29 Super Tucano a cewar ministan shine baza a sayar da jiragen ba har sai shekarar 2020.

Kuma ƙwararru masu gyara ƴan Najeriya baza su samu horo ba daga takwarorinsu na ƙasar Amurika ba ko kuma suka sance cikin mutanen da za su riƙa duba lafiyar jiragen 

Amma da yakewa ƴan jaridu jawabi Dan-Ali yace “waɗannan sharuɗa baza mu amince da su ba.”

Ya ƙara da cewa gwamnatin tarayya na shirin ganawa da jakadan ƙasar Amurika a Najeriya don ganin a rage wasu daga cikin sharuɗan.

You may also like