Gwamnatin tarayya za ta gurfanar da kamfanoni 30 a gaban kotu 


Kamfanoni 30 za su fuskanci tuhuma a gaban kotu kan rawar da suka taka a aikin gina katafaren titin nan da zai haɗa yankunan kudu da maso  gabas da kudu maso yamma da kuma a  sauran kwangiloli da  aka bayar  a ma’aikatar cigaban yankin Neja Delta da gwamnatin da ta gabata ta bayar.

Ministan kula da Harkokin  Yankin Neja  Delta, Pastor Usani Uguru shine ya bayyana haka a ranar Laraba lokacin da yake ganawa da manema labarai bayan taron majalisar zartarwa ta tarayya.

Ministan yace za a turawa Hukumar Yaƙi Da Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta EFCC sunayen kamfanonin domin ta gurfanar da su a gaban kotu.

Tun farko, Uguru ya fadawa yan jarida cewa an tsara gina titin ne na yankin Gabas zuwa Yamma akan kada a samu nasarar aiwatar da shi.

You may also like