Gwamnatin Tarayya Zata Gina Kotuna A Gidajen Yari


danbazau

Gwamnatin tarayya zata gina Kotuna a gidajen yarin dake ƙasarnan,domin hanzarta gudanar da shari’a, Ministan cikin gida Abdurrahaman Danbazau ne ya bada hasken haka yau a Abuja, Lokacin da yake ƙaddamar da motocin aiki 239 da kuma kayayyakin amfanin gona da hukumar kula da gidajen yarin ƙasarnan ta siya.

Dambazau yace yunƙurin yana da amfani wajen rage cinkoso da ake fama dashi a yawancin gidajen yarin dake cikin biranen ƙasarnan.

Lokacin da yake bayyana rashin jin ɗaɗinsa kan yadda kaso 72 cikin 100 na waɗanda suke zaune a gidajen yarin ƙasarnan sun zaman jira shari’a ne,yace aikine mai wahalar gaske ace hukumar sai ta kai ɗaurarru sama da 50,000 zuwa kotuna daban-daban dake watse a faɗin ƙasarnan a ko wacce rana.

“Tafiyar hawainiyar da tsarin shari’a yake a ƙasar nan da kuma daɗewar da muatne suke a ɗaure kafin a fara yi musu shari’a, ya janyo cunkoson gaske a galibin gidajen yarin da ke biranen ƙasarnan”

“Matsalar ta sake ta’azzara saboda ƙarancin ababen hawa da gidajen yarin suke dasu, daza a kai masu laifi  kotu a lokutan da yadace, wanda hakan yake sa ɗaurarrun su ƙosa da kuma kokawa kan halin da suke ciki” yace

Ministan yace irin wannnan yanayi ba abune mai karɓuwa ba a gurin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari , wanda yabada umarnin siyan motocin da kuma kayan aikin gonar.

Tun farko a jawabinsa shugaban hukumar kula da gidajen yari ta ƙasa Ja’afaru Ahmad ya yabawa gwamnati kan siyan motocin da kuma kayan aikin gonar, inda yace hakan zai kawo ƙarshen rashin jin daɗin aiki da ya addabi gonakin da hukumar ta mallaka.

You may also like