Gwamnatin Tarayya Zata Samar Da Makarantun Matan AureGwamnatin tarayya zata samar da makarantu domin matan da suka bar makaranta sukayi aure.Ministar harkokin mata Hajiya Aisha Jummai Alhasan, ta bayyana haka. 

“Duk matan da sukayi aure suna da karancin shekaru, zasu samu damar cigaba da karatu a gidajen mazajensu. 

“makarantun zasu kasance iri biyu saboda kada a samu matsala wajen kafa su. 

” Kason farko itace makarantar wadanda suka fara karatu amma wani dalili yasa suka dena. 

“Daya kason kuma itace makarantar koyar da karatun manya da za a bude a dukkanin kananan hukumomi dake fadin kasar nan domin taimakawa mata sukai wani matsayi na karatu da rubutu. 

” A makarantar karatun manyan za a koya matan sana’o’i, kamar su yin sabulu, dinki,yin kayan kwalliya da sauran kananan sana’o’i,” ministar ta bayyana haka ga manema labarai ranar Alhamis a Katsina. 

Alhasan tayi kira ga malaman addini da kuma masu rike da masarautin gargajiya  da su cigaba da taimakawa kokarin da ake na kara yawan yara mata da suke shiga makaranta.

Tace ilimin yaya yana da matukar muhimancin gaske saboda haka shugabanni ya kamata su karfafawa iyaye gwiwa wajen tura yayansu makaranta. 

You may also like