Gwamnatin Tarayya Zata Tona  Asirin Barayin Gwamnati Bisa Umarnin KotuA Jiya Laraba ne wata babbar kotu dake legas karkashin Jagorancin Jostis Hadiza Rabiu Shagari Ta umarci gwamnati tarayya data bayyana sunayen berayen gwamnati kowa ya sansu. 

Ministan Shari’a Na kasa Mista Abubakar Malami ya shaida amincewar gwamnatin tarayyar ne ga manema labarai baya dan gajeren zama da sukayi da kwamitin dake da cewa akan al’amarin. 

Kotun ta bada umarnin cewa yana da kyau kowa da kowa yasan su waye barayin gwamnatin da ake ta yayatawa cewa sunyi baba-kere da dukiyar al’umma, sannan kuma yana da kyau asan adadin kudin da kowannen su ya sata. 

You may also like