Gwamnatin tarayya tayi alkawarin sakin daurarru 368 dake gidajen yarin Kano a matsayin wani ɓangare na shirinta na rage cinkoso a gidajen yarin kasarnan.
Babban lauyan gwamnati kuma ministan sharia, Abubakar Malami ya bayyana haka ranar Talata a Kano lokacin da mambobin kwamitin masu ruwa da tsaki na ƙasa kan rage cinkoso a gidajen yarin ƙasarnan ya kai ziyarar ban girma ga gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Malami ya godewa gwamnan kan yadda ya shiga sawun gaba wajen kiran a rage cinkoso a gidajen yari inda ya bayyana cewa Kano ce jiha ta farko a kasarnan da ta karbi shirin ta hanyar sakin daurarru da dama.
Ya lura cewa gwamnan ya yiwa fursunoni 500 a fuwa a lokacin da shugaban kasa Muhammad Buhari ya kai ziyarar aiki a jihar yanzu an kuma shirya sakin wasu 368 bayan da gwamnatin jihar ta biya tarar da aka yi musu.
Tun farko shugaban kwamitin kuma tsohon babban alkalin alkalai na birnin tarayya Abuja ya shawarci dukkanin masu ruwa da tsaki kan su bawa batun rage cinkoso a gidajen yari kulawar da ta kamata domin kulawa ga masu karamin karfi a cikin al’umma.
Gwamna Ganduje ya bayyana farin cikinsa kan yadda kwamitin ya zabi Kano cikin jerin jihohin farko da kwamitin ya ziyarta domin tabbatar da an rage cinkoso a gidajen yari kamar yadda shugaban kasa Muhammad Buhari ya umarta.
Ya kara bayyana cewa tun daga farkon gwamnatinsa zuwa yanzu, gwamnatin ta yiwa fursunoni 1500 afuwa da suka aikata ƙananan laifuka yawancinsu da aka daure saboda gaza biyan tara.