Gwamnatin Venezuela ta kaddamar da rabon abinci a kasar


 

Gwamnatin Venezuela ta kaddamar da fara wani gagarumin shirin rabawa ‘yan kasar abinci, tare da bayyana kwamandojin rundunar sojin kasar 18 da zasu kula da shirin.

Ministan tsaron kasar Vladmir Padrino Lopez ne ya tabbatar da hakan, yayin wata ganawa da yayi da manema labarai a babban birnin kasar.

Shugaban Venezuelan Nicolas Maduro, na fatan ganin shirin ya rage karancin abinci da ‘yan kasar ke fuskanta.

Karancin abinci da kuma hauhawar farashinsa da mutanen kasar ke fuskanta ya haifar  da jerin zanga zanga a kasar ta nuna kin jinin gwamnatin Maduro wadda ba’aga irinta ba cikin shekaru sama da goma da suka gabata.

You may also like