Gwamnatin za ta sanar da karin albashi nan ba da jimawa-Ngige







Ministan ayyuka da kwadago, Chris Ngige ya ce nan gaba kadan gwamnatin tarayya za ta sanar da karin albashi ga ma’aikata domin rage radadin hauhawar farashin kayayyaki da ake fama da shi.

Ya fadi haka ne lokacin da yake ganawa da yan jarida a fadar shugaban kasa jin kadan bayan yayi ganawar sirri da shugaban kasa, Muhammad Buhari a Abuja.

Ya ce tuni kwamitin shugaban kasa kan albashi yake aikin sake duba albashin kuma ana sa ran zai fitar da rahoton sa a sabuwar shekara.






Previous articleTwo fun seekers drown in Lagos




Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like