Gwamnoni Sun Amince Su Rage Yawan Tawagar Dake binsu



A wani mataki na tsuke aljihun su sakamakon kariyar tattalin arziki, kungiyar gwamnonin Nijeriya (NGF) ta amince ta rage yawan kudaden da ‘ya’yanta ke kashewa wajen tafiyar da harkokinsu.
Da yake karin haske game da matakin kungiyar, Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i ya nuna cewa gwamnonin sun amince su rage yawan tawagar da ke binsu, da rage yawan tafiye tafiye da kuma takaita sanya tufafi na alfarma.

You may also like