Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje da takwarorinsa na jihohin, Jigawa, Osun, Ebonyi, Delta, Kebbi, Zamfara, Katsina, Sokoto da Kaduna sun gana da wani kamfanin noma na kasar China a ‘CAMALO’ a ofishin ministan noma Cif Audu Ogbeh.
Majiyarmu ta gano cewa an yi zaman ne tsakanin bangarorin biyu don kulla hadin guiwa domin samar da hatsi da rogo da alkama a jihohin.
Shirin dai zai taimaka wajen cimma muradin Gwamnatin tarayya na rage dogaro da man fetur wajen samun kudaden shiga zuwa komawa fannin noma da kiwo.