Gwamnonin APC suna goyon bayan shugabancin Oyegun- Yahaya Bello


Yahaya Bello, gwamnan jihar Kogi yace gwamnonin jam’iyar APC suna da ƙwarin gwiwa kan shugabancin jam’iyar ƙarƙashin jagorancin,  John Odigie Oyegun.

Bello wanda ya bayyana haka lokacin da yake magana da manema labarai  ranar Alhamis bayan da gwamnonin  suka gana da shugaban kasa Muhammad Buhari.

Bello na mayar da martani ne kan zargin da Bola Tinubu,jagoran jam’iyar na ƙasa ya yi cewa Oyegun yana masa zagon ƙasa a aikin sulhunta ƴan jam’iyar da shugaban ƙasa Buhari ya dora masa.

Amma Bello yace ya yin da yake goyon bayan kokarin sasanta ƴan jam’iyar wasu daga cikin ƴaƴan jam’iyar yakamata a hukuntasu.
“Mu gwamnoni da kuma yawancin ƴaƴan jam’iyar APC muna da ƙwarin gwiwa kan shugaban mu na ƙasa, John Odigie Oyegun,”ya ce.

Cikin zargin da Tinubu yakewa Oyegun ya haɗa da zuwansa jihar Kogi inda ya halarci bikin bude ofishin kar’ar ɓangaren dake biyayya ga gwamnan jihar Yahaya Bello.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like