Rahotannin daga Kaduna sun tabbatar da cewa a halin yanzu gwamnonin Arewa suna taro kan matsalolin rikice rikice da ke addabar yankin wanda ya hada da rikicin makiyaya da manoma.
Shugaban Kungiyar gwamnonin Arewa, Gwamnan Borno, Kashim Shettima ya ce a matsayinsu na zababbun shugabannin yankin dole sun nemo hanyoyin kawo karshen wadannan rikice rikicen.