Gwamnonin Arewa Sun Amince Da Tsige Sarkin Kano


Rahoton Daily Nigerian

A ƙalla Gwamnonin Arewa shida ciki har da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Ganduje sun hadu a Guangzhou, a ƙasar Chana, inda suka cimma yarjejeniyar daukar “mummunan mataki”: akan Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II. Zaman taron da shugaban Inuwar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya jagoranta sun cimma matsaya bayan doguwar muhawara a Ritz Carlton Hotel ranar Lahadi da ta gabata. 

Majiya ta ruwaito cewa, nan take wasu Gwamnonin suka goyi bayan cire Sarki Sanusi II yayin da wasu Gwamnoni biyu suka goyi bayan a Binciki kuɗaɗen asusun Masarautar Kano da wasu suka yi zargin Sarkin ya yi Wadaƙa da su. 

Gwamnonin sun amince cewa matukar aka ƙyale Sarki Sanusi II haka siddan ba tare da daukar mataki akan sa ba zai ci gaba da ragargarzar Gwamnonin. Don haka a kawar da shi a kawo wanda zai karbu a wajen talakawan jihar Kano. 

Gwamnonin da suka halarci zaman sun hada da Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, Gwamnan jihar Sakkwato Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, Gwamnan jihar Neja Abubakar Bello, Gwamnan jihar Nassarawa Tanko Almakura da kuma Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

You may also like