A yau Juma’a ne, Gwamnonin jihohin Kaduna, Malam El Rufa’i, Kano, Umar Ganduje, Niger, Abubakar Sani, Adamawa, Jubrilla Bindow, Kogi, Yahaya Bello, Yobe, Ibrahim Geidam suka tsayar da Shugaba Muhammad Buhari a matsayin dan takarar Shugaban kasa a 2019.
Gwamnonin sun cimma wannan matsayin ne bayan sun halarci Sallar Juma’a da Buhari a fadarsa inda Gwamnan Kaduna, Malam El Rufa’i ya jaddada cewa Buhari dan Nijeriya ne kuma yana da ‘yancin sake tsayawa takara idan har yana sha’awar yin hakan.