Gwamnonin Arewa Sun Yabawa Buhari Kan Nasarar Da Ya Samu Kan Yan BokoHaram 



Kungiyar gwamnonin Jihohin Arewa karkashin jagorancin Shugaban Kungiyar Gwamnan Jihar Borno Kashim Shatima, sun yaba gami dayin jinjina ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari, sakamakon kyakkyawar nasara da gwamnatinshi ta samu wajen kawar da Kungiyar ta’adda ta Boko Haram a fadin kasar nan, da kuma samar da ingantaccen tsaro a dukkanin kasa baki daya. 
Bayanin haka na kunshe ne a cikin takardar bayan taro na kwanaki biyu da Kungiyar gwamnonin suka gudanar hadi da Majalisar Sarakunan Arewa Karkashin shugabancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi Dakta Sa’adu Abubakar wanda ya gudana a fadar gwamnatin Jihar Kaduna ta Sir Kashim Ibrahim dake tsakiyar garin Kaduna. 
Gwamnonin sun bayyana cewar ya zama wajibi suyi jinjina ta musanman ga Shugaban Kasar, sakamakon rawar gani daya taka wajen dawo da Kasar akan saiti cikin kankanin lokaci. 
Gwamnonin na Arewa sun kuma lashi takobin sake inganta dukkanin kayan gado da yankin arewa ya gada daga Firimiyan Arewa na farko kuma na Karshe Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, abubuwa kamar kamfanin jaridar New Nigeria, da Ma’aikatar NNDC da Bankin Arewa, da sauran abubuwan cigaba wadanda Sardauna ya samar a lokacin rayuwarshi. 
Hakanan Kungiyar Gwamnonin na Arewa sun yaba da irin cigaban da gidauniyar Sardauna ta samu, wato Ahmadu Bello Memorial Foundation ta samar, wajen daukar nauyin dalibai ‘yan asalin yankin Arewa domin karo ilimi mai zurfi, da kuma bada gagarumin tallafi ga jama’a masu karamin karfi wajen kula da lafiya kyauta, sannan gwamnonin sun Yaba da kokarin kungiyoyin cigaban yankin Arewa kamar Kungiyar dattawan Arewa ta ACF da kuma da kuma Kungiyar manyan Arewa wato Northern Elders Forum, da kuma Majalisar Sarakunan Arewa. 
Gwamnonin Arewan sun koma mika ta’aziyya da jajantarwarsu ga gwamnatocin Jihohin Borno da Kaduna, sakamakon hatsarin daya faru a sansanin ‘yan gudun hijira dake Rann karamar hukumar Kala Balge dake jihar Borno na tashin bom bisa ga kuskure da aka samu, da kuma bala’in dake faruwa a yankin kudancin Kaduna.

You may also like