Gwamnonin Arewa Zasu Farfado Da Bankin Arewa-Ganduje 


Gwamnonin Arewa 19 sun fara wani yinkuri na tara kudi domin ceto Bankin Arewa daga halin da yake ciki a shekarun da suka gabata ne aka hade bankin da wasu cibiyoyin kudi domin habaka jarinsa. 

Gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje shine ya bayyana haka lokacin da yakewa majalisar zartarwar jihar jawabi.

Ganduje yace gwamnonin yankin 19 sun cimma wannan matsaya ne a wani taro da sukayi a Kaduna.

 Yace bayan shirin farfado da Bankin Arewa,gwamanonin sun amince da farfado wasu fannoni na tattalin arziki da suka hada da masakun da suka durkushe  a wasu jihohi dake yankin. 

A cewarsa  gwamnonin sun tattauna sosai akan matsalar rikicin manoma da makiyaya.

Gwamnan yace gwamnonin sun kuma tattauna bukatar samun hadin kai,zaman lafiya da kuma cigaba me dorewa a yankin. 

You may also like