
Asalin hoton, .
Gwamnonin da suka samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu
A ranar Asabar 18 ga watan Fabrairu aka gudanar da zaɓen gwamnoni da kuma na ƴan majalisun dokoki na jihohi a Najeriya.
Yayin da aka sanar da sakamakon wasu jihohi, wasu kuma ana ci gaba da tattara sakamakon.
Ga jerin gwamnoni da suka yi tazarce a kan kujerunsu a zaɓen da aka gudanar.
Babban jami’in tattara sakamakon zaɓe na jihar Legs, Professor Adenike Temidayo Oladiji ya bayyana gwamna ma ci Babajide Sanwo-Olu a matsayin wanda ya samu nasarar komawa kan mulki karo na biyu.
Sanwo Olu ya samu nasara ne da ƙuri’u 762,134.
A jihar Gombe ma, hukumar zaɓe ta hannun jami’ar tattara sakamakon zaɓen gwamna a jihar, Farfesa Maimuna Waziri ta ayyana Inuwa Yahaya a matsayin wanda ya yi nasarar sake ɗarewa kan mulki da kuri’u 345,821.
Hukumar zaɓe a jihar Kwara, ta ayyana gwaman mai ci AbdulRahman AbdulRazaq a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamna.
AbdulRahman ya koma kan mulki ne bayan samun nasara a illahirin kananan hukumomi 16 na faɗin jihar.
A jihar Yobe ma, gwamna Mai Mala Buni ne ya samu nasarar komawa kan karagar mulki.
Mai Mala Buni ya samu nasara ne da kuri’u 317,113, inda ya doke abokin karawarsa Sheriff Abdullahi na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 104,259.
Gwamna Seyi Makinde na jam’iyyar PDP, shi ya lashe zaɓen gwamnan jihar.
Makinde wanda shi ne gwamna mai ci ya samu ƙuri’u mafi yawa inda ya bai wa babban ɗan adawa a jihar, Teslim Folarin na Jam’iyyar APC tazarar ƙuri’u kusan dubu 300.
A can jihar Ogun ma, gwamna Dapo Abiodun ne ya ci zaɓen gwamnan jihar da da aka yi a ranar Asabar.
Ya samu nasara a karo na biyu ne bayan samun kuri’u 276,298, inda ya doke abokin hamayyarsa Ladi Adebutu na jam’iyyar PDP wanda ya samu ƙuri’u 262,383.
A jihar Nasarawa ma, hukumar zaɓe ta sanar da gwamna mai ci Abdullahi Sule a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen gwamnan jihar.
Jami’in tattara sakamako zaɓen gwamnan jihar Ishaya Tanko, shi ya sanar da hakan a Lafiya babban birnin jihar.
Abdullahi Sule ya samu damar komawa kan karagar mulki ne da kuri’u 347,209.
Gwamna Bala Muhammad na jihar Bauchi ya sake ɗarewa kan mulki karo na biyu a sakamakon zaɓen gwamna da aka sanar a ranar Litinin.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Abdulkarim Sabo Mohammed ya ce Bala Ƙaura ya samu nasara ne da ƙuri’u 525,280.
Ya doke babban abokin hamayyarsa Air Marshal Abubakar Sadique Baba na jam’iyyar APC wanda ya samu ƙuri’u 432,272.