Gwamnonin Gombe, Bauchi Sun Samu Wa’adi Na Biyu
An sake zaban gwamnonin Bauchi da Gombe a wa’adi na biyu, biyo bayan zabubbukan gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata.

Gwamna Bala Abdulkadir Muhammad, wanda ya yi takarar karkashin tutar jam’iyyar PDP mai alamar lema ya lashe zaben da 525,280.

Wakilin Muryar Amurka, Abdulwahab Muhammad ya tattauna da mataimakin shugaban Jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutse, shalkwatar jihar Jigawa Farfesa Abdulkarim Sambo wanda ya kasance babban baturen zabe a jihar Bauchi.

Mawaka magoya bayan jam’iyyar sun nufi kofar gidan Ramat mallakin gwaqmnati domin nuna farin cikin su.

Shi ma gwamnan jihar Gombe makwabciyyar jihar Bauchi Mallam Muhammad Inuwa Yahaya na jam’iyyar APC ya lashe zaben gwamna a jiharsa da kuri’a 342,821.

Mataimakiyar shugaban jami’ar Gashua da ke jihar Yobe Farfesa Maimuna Waziri ce ta bayyana sakamakon zaben a harshen turanci.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like