Gwamnonin jihohin arewa da dama sun fada min za su kori malamai bayan zaben shekarar 2019- El-rufa’i


Nasir El-rufa’i,gwamnan jihar Kaduna ya ce da dama daga cikin gwamnonin dake jihohin arewa za su kori malamai bayan zaben shekarar 2019.

A cewar jaridar Punch, El-rufa’i ya bayyana haka lokacin da ya kasance babban bako mai jawabi a jami’ar kimiyyar aikin likita dake jihar Ondo.

A farkon wannan shekarar ne gwamnan ya shiga kaddamar da kawo wani gagarumin sauyi a bangaren ilimi da ta kai ga ya kori malaman makarantun firamare 21000.

El-rufa’i, ya ce bayan ya dauki matakin yawancin takwaran aikinsa da suka fito daga arewa sun sheda masa cewa abinda ya yi dai-dai ne.

Basu da kwarin gwiwar yin haka kafin zaben.

“Muna da kungiyar gwamnoni daban-daban a kasarnan, muna da Kungiyar Gwamnonin Arewa inda muke musayar bayanai.Zan iya fada muku da yawa daga cikin abokanan aikina daga jihohin arewa sun fada min cewa abinda nake dai-dai ne,”ya ce.

“Sun fada min cewa suna da gagarumar matsala makamanciyar haka a jihohinsu amma ba za su iya yin komai akai ba. Ina tunanin bayan zabe mai zuwa za ku ga sauye-sauye da dama suna faruwa saboda da yawa daga cikin gwamnonin za su yanke shawarar yin irin haka.”

You may also like