Gwanman Jihar Kaduna Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudin 2017Gwamnan Kaduna, Malam Nasir El Rufa’i ya rattaba hannu a kan kasafin kudin shekarar 2017 wanda majalisar dokokin jihar ta amince da shi wanda aka tsara kashe Naira Bilyan 214.9.
A yayin da yake rattaba hannu kan kasafin, El Rufa’i ya ce gwamnatin jihar ta samu tallafi daga gwamnatin tarayya wanda za ta yi amfani da kudaden wajen biyan basussuka ‘yan Fansho na kusan shekara shida da kuma hakkokin ma’aikatan da suka yi ritaya da kuma wadanda suka mutu.

You may also like