Gwannatin Tarayya Za Ta Fara Aikin Hako Danyen Mai a Jihar Bauchi. 


…za mu gina muhalli kyauta ga ma’aikatan da za’a turo, inji Gwamnan jihar
Gwamnatin tarayya tace nan bada jimawa ba za’a fara aikin hako danyen man fetur a jihar Bauchi. Bayanin hakan ya fito ne daga manajin Darkta na hukumar NNPC, Dr. Maikanti Kacalla Baru a lokacin da ya ziyarci Gwamnan jihar Bauchi M. A. Abubakar a ofishinsa.
Yana mai cewa akwai kyakkyawan zaton cewa za’a samu ingantaccen danyen albarkatun mai a jihar duba da yadda jiyar ke makwaftaka da tafkin Chadi.
Dakta Baru yace tuni NNPC ya bude sashin na musamman a jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da jami’ar Modibbo Adama dake Yola domin bada horo na musamman ganin cewa aikin zai bunkasa tattalin arzikin jihar kana zai samar da dumbin ayyukan yi ga matasa.
Tun da farko Mista Baru yace makasudin ziyarar Gwamnan shine domin yaba masa bisa goyon bayan da yake baiwa kamfanin na NNPC wajen ganin aikin hako man ya kankama.
A nashi bangaren Gwamnan Bauchi,  M.A Abubakar ya yaba da ziyarar tare da yiwa kamfanin na NNPC albishir cewa Gwamnatinsa ta dauki alkawarin gina muhalli ga dukka ma’aikatan da kamfanin zai turo domin aiki a jihar.
A cikin sanarwar da maitaimakin Gwamnan a fannin sadarwa Shamsudden Lukman Abubakar ya fitar yace Gwamnan na kuma bakin kokarinsa domin bunkasa sauran fannonin da suka hada da Noma da Kiwo da Masana’antu da kawata gandun jihar don masu zuwa yawon bude ido.

You may also like