Gwarazan Shekara Na Shekarar 2016


Hakika kowace shekara tana da abun da ba za’a manta da ita ba, tana da wadanda ba za a manta da ita ba saboda abunda suka yi, tana kuma da munanan abubuwa da baza’a manta da it aba saboda aukuwan su. Kamar kowace karshen shekara, wannan karo ma na fitar da gwarazan shekara na 2016. Gwarzo daya ne ban fitar ba kaman yanda na saba shine gwarzon malami ba don babu ba sai saboda ban gama tantancewa ba. Ina fata zaku ji dadin karantawa.
GWARZON SHEKARA MAFI BAN TAUSAYI
Isa Hamma, matashi ne da wani likita ya cire wa koda ba bisa ka’ida ba a asibitin Jimeta, a cikin garin Yola fadan jihar Adamawa. Babu shakka wannan bawan Allah ya sha azaba kuma yana cigaba da shan azaba sakamakon sakacin likitan wanda ya cire mishi koda duka biyu. Sanadiyyar hakan likitoci suka sanya Isa Hamma akan na’ura saboda bashi da daman cin abinci, ya dau watanni a asibitin tarayya (FMC) a Yola kafin sannan aka wuce dashi asibitin malam Aminu Kano a bisa cewa gwamnan jihar Adamawa ya dauki nauyin za’a yi mishi aiki na sanya koda. Wani matashi ne ya dau nauyin bada kodar sa daya kyauta saboda Isa Hamma ya rayu.
SABODA ILLAN DA AKA YI MISHI DA KUMA HALIN NI ‘YASU DA YA SHIGA A RAYUWA, ISA HAMMA YA KASANCE GWARZON SHEKARA NA MAFI BUKATAR TAUSAYA WA.

 


JARUMIN SHEKARA 
Marigayi Laftanar Kanal Abu-Ali jarumin soja ne na kasar Nijeriya da ya rasa ransa yayin wani hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai sansanin su na sojoji a ranan jumma’a 04 ga watan Nuwamba cikin wannan shekarar ta 2016. Bayan wannan hari da aka kai wanda yayi sanadiyyar rasuwar Kanal Abu Ali (Allah ya jikan shi), duniya ta dauka da labrin jarumtar shi inda aka bayyana shi a matsayin daya daga cikin jarumai da suka jagoranci yakin Boko Haram cikin rundunar sojoji. Kanal Abu Ali wanda shugaban hafsan sojojin Nijeriya Janar Tukur Buratai ya yi mishi Karin girma saboda hazakan sa, da ne ga wani basarake a jihar Neja. Uba ne ga yara biyu kuma miji ne ga mace daya.

SABODA JARUMTAR DA YA NUNA WAJEN KARE KASAR SHI, SABODA SADAUKAR DA RANSHI DA YAYI DON SAMUN ZAMAN LAFIYA A KASAR SHI, SABODA GUDUNMAWA MARA MISALTUWA DA YA BADA WAJEN YAKAR BOKO HARAM, LAFTANAR MUHAMMAD ABU-ALI YA KASANCE JARUMIN SHEKARA NA.
GWARZON LABARI
Labaru suna da dama wadanda suka faru a cikin wannan shekara amma labari daya ne ya sha gaban kowanne a tarihin kasar mu Nijeriya. Labarin kuwa shine nasarar kore ‘yan ta’addan Boko Haram daga babban cibiyan su a dajin Sambisa. Kungiyar Boko Haram babu shakka tayi wa kasar nan illa a baza’a ta ba mantawa ba. Tarihi ya dauka kuma alkalami ya bushe, cewa ba’a taba samun ‘yan ta’adda da suka illata al’umma Kaman miyagun mayakan Boko Haram ba. 
A karkashin gwamnatin da ta gabata na Goodluck Jonathan, kungiyar ta ci Karen ta babu babbaka inda tayi nasarar fatattakan mutane daga gidajen su kuma suka kafa tuta a garuruwa da dama. A wancan lokaci Boko Haram ba’a daji suke ba, suna cikin gari ne suna gudanar da ta’addancin su a fili. Da zuwan shugaba Buhari ya mai da akalar gwamnatin sa akan kawo karshen wannan bala’i. wannnan yakai ga kwato mutane da dama da kungiyar tayi garkuwa da su tare da yakar kungiyar. Babban nasara da gwamnatin Buhari zata yi alfahari dashi shine kore ‘yan ta’addan Boko Haram daga Sambisa. Ba kuma Buhari kadai ba, duk wani dan Nijeriya wannan babban abun farinciki ne a gare shi.

SABODA GIRMAN LABARIN DA KUMA DADIN SHI GA DUKKAN AL’UMMAN KASAR NAN TA NIJERIYA, LABARIN KORE ‘YAN BOKO HARAM DAGA DAJIN SAMBISA YA ZAMA GWARZON LABARI NA A WANNAN SHEKARAR.
MUMMUNAN LABARI
A ranar Alhamis 28 ga watan October dakarun tsaron Saudiyya suka dakile wani makami da ‘yan tawayen Hauti suka aika zuwa kasar ta Saudiyya wanda masana suka ce makamin an aika shi ne kai tsaye zuwa Makka, inda dakin kaba yake.
Dakarun Saudiyya sun bayyana cewa sun dakile makamin kuma sun tarwatsa shi kilomita 65 daga makka. 
SABODA MUNIN LABARIN, WANDA IDAN DA MAKAMIN YA ISO MAKKA YANDA ZATA KASANCE, WANNAN LABARI YA KASANCE MAFI FIRGITARWA DA MUNI A WANNAN SHEKARAR.
GWARZON GWAMNA
Gwamna Umaru Jibirilla Bindow na jihar Adamawa a cikin kankanin lokaci ya sauya jihar zuwa daya daga cikin manyan jihohi ta hanyan kawo wa jihar cigaba masu yawa. Duk wanda ya dau lokaci da shiga jihar Adamawa musamman birnin Yola da kewaye, to idan ya shigo duk kiyayyan shi da gwamna Bindow sai ya jinjina mishi. Jihar ta samu shimfidaddun hanyoyi wadanda ba’a taba yin irin su ba a tarihin jihar.
Bani da wani alaka ko kadan da gwamna Bindow, asali ma nayi rubuce rubuce akan cewa bai dace da mulkin jihar nan ba a baya. To amma daga baya nazo na yi rubutu cewa an samu gwamna da tarihi bazata taba mantawa dashi ba. Duk da cewa ni dan jihar Adamawa ne ban taba ko da hira na aikin jarida da shi ba. Watanni kadan hakan yaso ya faru amma sai aka sauya ni zuwa wani aikin. Amma gwamna Jibirilla Bindow mutum ne mai matukar saukin kai da kuma son shiga talakawa. Ni da kaina na sha ganin shi yana yawo a cikin Yola da mota daya tal yana duba ayyukan da ake yi! 
Tarihi ya nuna cewa tun da aka kafa jihar Adamawa ba’a taba samun gwamna da ya gabatar da zaman majalisar zartaswa ta jihar a wajen fadan jihar. To amma gwamna Bindow yakan gabatar da zaman ne tare da mukarraban shi a kananan hukomi mabanbanta. Idan yau yayi a nan, to gobe a can zai yi. Duk inda yaje sai ya gana da dalibai, sarakuna da kuma masu mulki.
SABODA FIFITA BUKATUN JIHAR ADAMAWA A KAN BUKATUN SHI, SABODA SAKA CIGABAN JIHAR ADAMAWA A MATSAYIN BABBAN MURADIN SHI, GWAMNA JIBIRILLA BINDOW YA KASANCE GWARZON GWAMNA NA A WANNAN SHEKARAR. 
BASARAKEN SHEKARA

Mai Martaba Sanusi Lamido Sanusi, sarkin Kano, magajin Ado Bayaro, tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya ya kasance sarki mafi daukan hanakali a wanan shekarar. Mutum ne da yake da ilimin addini gwargwadon hali, da ilimin boko iya abun da ya kamata kuma Allah ya mai sarautar jihar Kano. 
Abu mafi daukan hankali a game da gwarzon nawa shine tsayuwan shi sosai wajen bawa wannan gwamnati na Shugaba Buhari shawara akan abubuwa da dama. Wasu sun bada shawarar cewa da SLS ya bada shawarar shi ba tare da bayyana su ba. Ni kuwa a nawa ganin, gwarzon nawa koda ya bada shawarar a boye, yana kuma dacewa ya fito fili ya bayyana wa gwamnati saboda ai ba shugaban kasa bane kadai a gwamnati. 
Abun da zamu fahimta shine wadannan shawari da ake cewa ya bayar ba kiran manema labaru yake ba yayi taro ya bada su, galibi yakan bada su ne a yayin gabatar da kasidu a taruka mabanbanta. To idan abun ta fado akan gwamnati, dole ne yayi magana kasancewar sa shugaban al’umma bawai yayi shiru ba.
SABODA TSAYUWAR SA AKAN GASKIYA DA KUMA KOKARIN SHI NA BADA GUDUNMAWA WAJEN GINA KASAR NAN, MAI MARTABA SANUSI LAMIDO SANUSI II, SARKIN KANO, YA ZAMA GWARZON BASARAKE NA A WANNAN SHEKARAR.
 Wadannan sune fitattu cikin gwarazan shekara na duk da cewa akwai su da dama. Hakika sun ja hankali na sosai a wannan shekara. ina fata su kasance cikin ayyukan yabawa ga al’umma, wadanda suka rasu kuma Allah ya jikan su, wandanda basu da lafiya kuma Allah ya basu lafiya.

You may also like