Firaminstan Habasha Abiy Ahmed ya lashe zaben ‘yan majalisun dokokin da aka gudanar a kasar da gagrumin rinjaye kamar yadda hukumar zaben kasar mai zaman kanta ta bayyana.
Hukumar zaben ta ce Aby Ahmed ya samu kujeru 421 daga cikin 436 na kujerun ‘yan majlisun kasar, lamarin da ka sake bashi wata dama na ci gaba da tafiyar da mulkin Habasha.
Sai dai zaben na 12 ga watan Yuni, ya fuskanci wasu tarin kalubalai na tsaro a yankunan kasar da dama, musamman yankin Tigrey inda a ya zo daidai lokacin da ake fafatwa tsakanin ‘yan tawayen yankin da dakarun gwamnati, kafin cimma matsaya kan tsagaita wuta a karshen watan Yuni.