Hoton dai ya taimaka wajen karfafa zargin yiwuwar kaddamar da munanan hare-hare a kan ‘yan tawayen yankin na Tigray da ke rikici da gwamnatin Habashan tun a shekara ta 2020, rikicin kuma da aka kiyasta ya janyo asarar rayukan mutane imanin 1000. Wasu rahotanni na nunar da cewa, an hada kan ma’aikatan gwamnati da dalibai a Iritiriyan domin a tura su filin daga. Kasar Iritiriya dai ta hada kai da gwamnatin makwabciyar kasa Habasha, domin yakar ‘yan tawayen na yankin Tigray tare da musanta duk waasu zarge-zarge na cin zarafi da ake wa sojojinta. Ko da a makon da ya gabaata ma dai, sai da ‘yan tawayen na Tigray suka zargi mahukuntan Iritiriya da kaddamar da munanan hare-hare a kan iyakar.