Hada-hadar Kasuwanci Da Zawarcin Zaratan ‘Yan Wasan Kwallon Kafa Na Duniya


Wata takaddama na neman kunno kai a hukumar kula da kwallon kafa ta Nigeria (NFF), bayan sanarwar da hukuma ta bayar jiya na zaben Paul Le Guen a matsayin sabon mai horas da yanwasan super Eagles na Nigeria.

Sabon mai horas da ‘yan wasan Super Eagles din ya bukaci hukumar data yardar masa ya koma kasar sa ta Faransa da zama. Paul yace zai zauna a Faransa Amman zai rika zuwa Najeriya yana komawa, yayinda ita hukumar ta ki amincewa da bukatar tasa.

Sai dai kawo yanzu ba’aji tabaki Le guen ba akan rashin amincewar da hukumar tayi ba.

Kungiyar kwallon kafa ta Man Utd na dab da sayen dan’wasan kungiyar Juventus maisuna Paul Pogba akan zunzurutun kudi har yuro miliyan €125, Kimani Fan miliyan £104, Kenan, inda Pogba zai rika daukar kudi yuro miliyan €12, duk shekara .

Pogba zai iya kasancewa dan’wasan da yafi kowane dan’wasan kwallon kafa tsada a kakar wasannin bana. Pogba ya bar Man Utd a 2012 a matsayin kyauta wato (free transfer) ya koma kungiyar Juventus.

Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Leicester City ta sa kudi Fan miliyan £45, ga duk wani mai bukatar dan’wasanta mai suna Riyad Maharez dan shekaru 25, da haihuwa.

Chelsea na neman mai tsaron gida na AC Millan Diego Lopez mai shekaru 34, da haihuwa, yayin da ita kuma Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid na zawarcin danwasan velancia mai suna Andre Gomes dan shekaru 22, da haihuwa akan kudi Fan miliyan £50.

Yayinda kungiyar kwallon kafa ta chelsea ke kira ga Kungiyar kwallon kafa ta Atletico Madrid da ta janye daga neman dan’wasanta maisuna Diego Costa, inda kungiyar chelsea tace ba nasayar wa bane.

Itama Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal ta bukaci Kungiyar kwallon kafa ta Man City, da ta hakura da neman danwasanta maisuna Hector Bellerin dan shekaru 21, da haihuwa Kungiyar ta Arsenal ta ce baza ta rabu dashi nan kusaba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like