An Haifi Yaro na Farko mai Iyaye 3 a Duniya


 

A kasar Mexico, an haifi da na farko a duniya mai iyaye uku ga wasu ma’aurata ‘yan kasar Jordan.

‘Dan wanda aka haifa watanni 5 da suka wuce na dauke da kwayoyin halitta na mutane 3, kuma yanzu haka yana nan cikin koshin lafiya, inji wani rahoto da aka wallafa a mujallar kimiyya ta ‘New Scientis Magazine’ a jiya Talata.

Mahaifiyar yaran na dauke da wata cuta mai suna ‘Leigh Syndrome’ wanda ta shafawa ‘yayanta guda biyu na baya, wadanda cutar ta kashe, banda haka cutar ta sanyata ta yi bari har sau hudu.

A dan haka ne matar da mijinta wadanda ba’a bayyana sunansu ba suka nemi taimakon wani likita mai suna John Zhang wanda ya cire bangaren da ke da cutar a kwan matar, ya dasa na wata matar. Wannan ya bayarda damar haihuwar yaro wanda ke da kwayoyin halittar iyayen amma ba ya dauke da kwayar cutar.

Tunda kasar Amurka ba ta yarda da irin wannan salo na haihuwa ba, likita John Zhang ya fita kasar Mexico inda a nan ya kammala komai.

Ana fatan cewa ‘dan zai girma ya yi rayuwa cikin koshin lafiya.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like