Hajj2016- Alhazai a Filin Arfa


A yau ne miliyoyin musulmai da ke gudanar da aikin hajji suke tsayuwar Arfa, wadda ita ce rukuni mafi girma a aikin Hajjin.
Tun jiya Asabar ne dai alhazan suka fita filin Mina da ke wajen garin Maka, inda daga nan kuma suka wuce filin na Arfa, sannan da yamma su kama hanyar zuwa Muzdalifa, su wayi gari, sannan su koma Mina domin fara jifa.

Mahajjatan sun taru a filin Arafa, inda Annabi Muhammad SAW ya gabatar da hudubarsa ta ban kwana.

Mahajjatan dai za su shafe wuni suna addu`a`i da karatun alkur`ani.

A bara dai an samu hadari a kusa da wajen jifa, wato Jam`rah, inda sama da mutum 2000 suka rasu, kuma alhazan kasar Iran ne suka fi yawa daga ciki.

Wannan ne ya sa al`umar Iran din suka ki zuwa aikin hajjin bana, har ma sun shirya wata hidima a birnin Karbala da ke Iraki, a ranar Asabar

You may also like