Hajj2016 –  An kama ‘yar Najeriya da hodar ibilis


Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA ta ce ta kama wata mata dauke da hodar Iblis a kan hanyarta ta zuwa kasar Saudiyya domin aikin Hajji.
Wata sanarwa da hukumar ta NDLEA ta fitar ta ce an kama Binuyo Basira Iyabo ne yayin bincike, a filin jirgin sama na babban birnin kasar Abuja, bayan da aka gano ta hadiyi hodar-Iblis mai dimbin yawa.

Tuni dai matar mai shekaru 55 ta yi kashin kwanso 76 na hodar iblis, sannan ana ci gaba da tsare ta don tabbatar da cewa ta fitar da dukkan kwayoyin da ta hadiya.

Matar dai tana shirin shiga jirgin Emirate ne, inda za tasauka a birnin Madina, bayan ta biya ta birnin Dubai na hadaddiyar daular Larabawa.

A cewar hukumar dai matar da ake zargi ta shaida mata cewa wani ne ya dauki nauyin ta dan safarar hodar-iblis din zuwa kasa mai tsarki.Ta ce mutumin kuma ya yi mata alkawarin biyan ta Naira miliyan daya.

Ko baya ga Basira Iyabo, hukumar ta NDLEA ta ce ta kuma kama wani mai suna Okpalanhem Henry wanda ake zargin sa da cusa hodar-iblis mai nauyin giram 355 a duburarsa.An kama mutumin, wanda dan Nigeria ne a filin jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Legas.

Shi dai Henry yana dauke ne da fasfo na kasar Mali da sunan Diara Saudou a inda yake shirin tafiya kasar Sin.Sanarwar ta NDLEA ta ce kama mutanen a gida Nigeria ya tseratar da su daga hukuncin kisa da za su iya fuskanta a kasashen biyu.

Kasashen Saudia da kuma Sin dai na yanke hukuncin kisa ne a kan duk mutumin da aka kama da laifin shigar da miyagun kwayoyi kasashen.

You may also like