Hajj2016 –  kawo yanzu ‘yan Najeriya 18 ne suka mutu. 


Hukumar Alhazan Najeriya ta ce kawo yanzu ‘yan kasar 18 ne, maza da mata, suka rasu, yayin aikin hajjin bana, a Saudiyya.
Shugaban hukumar ta alhazai, Abdullahi Mukhtar wanda ya shaida wa’ yan jaridu hakan, ya ce mutanen sun mutu ne sakamakon nau’in cututtuka daban-daban.

Sai dai kuma shugaban hukumar ya amince da gazawar shugabannin hukumomin alhazai na jihohi wajen tantance marasa lafiyar.

Ya kuma ce an fara jigilar alhazan kasar, ranar 17 ga Satumba, a inda jirage uku su ka fara sauka a filin jirgi na babban birnin kasar wato Abuja.

Malam Abdullahi ya kuma kara da cewa ana sa ran sauran jirage za su fara jigilar alhazan wasu jihohi, ranar 18 ga Satumba.

Shugaban na Hukumar Alhazan ya ce bana alhazan Najeriya ba za su zama kurar baya ba wajen jigila ba.

Dangane kuma da kayan alhazai, Mukhtar ya ce a bana karamar jaka daya tal aka yarjewa kowane alhaji shiga da ita jirgi.

Sannan kuma ba a yarda nauyin babbar jaka ya wuce kilo takwas ba. 

Karin bayani

A baya dai ‘yan Najeriya na mutuwa a kasar Saudiyya sakamakon hadurra iri daban-daban.

Wasu dai sun sha sukar Hukumar Alhazan kasar da gazawa wajen kiyaye alhazanta.

Har wa yau, babbar matsalar da alhazan Najeriya ke fama da ita, ita ce zama fiye da kima a filin jirgin domin dakon jirage zuwa gida.

Hakan ne ya ke sanya alhazai da dama kashe guzirinsu a filin jirgin saman.

Har ta kai wasu alhazan kan zauna a filin jirgin na ‘yan kwanaki.

You may also like