Hajj2017: An Kammala Jigilar Alhazan Najeriya Daga Kasa Mai Tsarki Yau ake kammala kwashe Alhazan Nijeriya rukunin karshe daga jihohin Rivers, Kebbi, Kano da wassu jami’an hukumar alhazan Nijeriya, jirgin Max ne ya ɗebo su daga ƙasar Saudiyya zuwa gida Nijeriya, Hakan ya alamta kammala jigilar alhazan kwata kwata a wannan shekara ta 2017.

Shugaban hukumar alhazan Nijeriya NAHCON Barista Abdullahi Mukhtar Muhammad ne ya zo don duba tantance alhazan da rakiyar karamin jakadan Nijeriya a Saudiyya Alh. Muhammad Sani Yunusa.

Mukhtar ya nuna farin ciki da yadda jigilar ta kawo karshe cikin nasara inda ya ce alhazai 6 kadai a ka bari a baya da ke samun magani a asibiti wadanda ofishin jakadanci zai ci gaba da duba su har su samu sauki don dawowa gida.

Barista Mukhtar ya godewa alhazan Nijeriya don addu’ar da su ka yi wa shugaba Buhari da kuma dorewar hadin kan kasar, yare da fatan Allah ya amshi dukkan ibadun da aka gabatar.

You may also like