Hajj2017: Yau Mahajjatan Najeriya Zasu Fara Dawowa GidaDaga Madina An kammala dukkan shirye shiryen da suka kamata domin fara jigilar mahajjatan Nijeriya zuwa gida, daga filin jirgin saman kasa da kasa na Muhammad Bn Abdulaziz dake Madina, inda ake sa ran farawa da mahajjatan Jihar Gombe. 

Tun da aka saukar maniyyata a filin saukar jirage na Madina a bana, mahajjata kalilan ne za a mayar kasashen su ta wannan filin jirgi, a maimakon babban filin jirage na Sarki Abdulaziz dake Jidda, wanda akasari nan ne aka saba jigilar mahajjata zuwa kasashen su. 

Shugaban hukumar kula aikin Hajji ta Nijeriya, NAHCON Barista Abdullahi Muhammad Mukhtar ya shaidawa manema labarai cewa irin shirin da ake yi na dawo da mahajjata, inda ya bayyana cewa, idan tsarin da ake so ya yiwu to, jirgin kasar Sa’udiyya na FLYNAS shi zai yi aikin jigilar dawo da maniyyata daga Madina. 

Shugaban ya ce, ana sa ran kammala dukkan aikin dawo da mahajjata gida a tsakanin 5 ga watan Oktoba mai zuwa, idan har ba a ci karo da wata tangarda ba. 

Ya kuma yabawa kokarin da ‘yan jaridu suke yi wajen sanar da al’ummar kasa halin da ake ciki, da yadda ayyuka ke gudana a kasa mai tsarki, tare da kira gare su da kada su yi sanyi wajen bayar da bayanan yadda ake gudanar da ayyukan kwashe alhazai.

Da yake nasa karin bayanin, kwamishinan kula da ayyuka na hukumar, Alhaji Abdullahi Saleh Modibbo ya bayyana cewa, tuni an sanar da dukkan kamfanonin jirage ukun da aka yi aikin jigilar da su tsarin da aka yi na kwasar alhazan. 

Ya kara da cewa, jirgin FLYNAS zai kammala aikin sa na kwashe alhazai ne tsakanin 7 ga watan Satumba zuwa biyu ga watan Oktoba, yayin da MedView zai kammala nasa tsakanin 10 da 25 ga wannan wata, sai Max Air da zai kammala nasa tsakanin 9 ga watan Satumba zuwa 5 ga watan Oktoba. 

Kwamishinan ya kara da cewa, hukumar na yin dukkan abin da ya kamata, domin ganin ba a samu wata tangarda ba. 

A nasa jawabin, kwamishinan kula da kudi da ayyukan ma’aikata, Alhaji Adebayo shi ma ya yi karin haske kan aikin auna kayan mahajjata, inda ya ce tuni aiki ya bada tabbacin cewa za a cigaba da aikin ciyar da mahajjata da zirga-zirgar su har sai mahajjata sun koma wajen iyalansu. 

Kawo yanzu dai mahajjata 14 ne tare da wasu ma’aikatan hukumar NAHCON suka rasa rayukan su a yayin aikin Hajjin bana. 

Kwamishinan kula da harkokin lafiya na hukumar, Dr Ibrahim Kana ya bayyana cewa, kimanin mahajjata dubu 18 ne ma’aikatan jinya suka duba lafiyar su, daga cikin su mahajjata dubu 6 an ba su magani a Mina da Arafat. 

A wani labarin kuma, hukumar kasar Sa’udiyya dake kula sarrafa naman hadaya da aka yanka, wanda bankin IDB ke kula da ita, ta fitar da sanarwar cewa, ‘yan Nijeriya sun yanka dabba 15,601, wanda aka biya kudaden su ta bankin Ja’iz. 

You may also like