
Asalin hoton, NAHCON
Saudiya ta dawo wa da Najeriya adadin kujerun da ta saba ba ta sama da 95, 000, na mutanen da za su je aikin Hajji a 2023.
Hukumar ƙasar ta Saudiya ta bayyana hakan ne a wata ganawa da hukumar alhazan Najeriya, a yau Laraba.
Suwaiba Ahmad, mai magana da yawun hukumar alhazan Najeriya ce ta tabbatar wa BBC matakin na Saudiya.
“Saudiya ta dawo da Najeriya kujerun da ta saba ba ta 95, 000, wanda a baya ta rage suka koma, 45, 000 saboda matsalar cutar korona, wanda shi din ma ba mu iya cikewa ba, saboda an bayar da shi a kurarren lokaci
Kazalika Saudiya ta ce an cire dokar taƙaita shekarun masu zuwa aikin hajji, da aka sa a aikin hajjin da ya gabata.
Sannan hukumar ta NAHCON ta ce a jiya Talata ƙasar ta Saudiya ta dawo da Najeriya Riyal 542, 033 kwatankwacin naira miliyan 107, 864, 567 na kudin abincin da aka sami matsala da kamfanin Mutawwaifs da ke kula da abinci mahajjatan da suka fito daga Afirka.
Saudiya ta dawo da kudin abincin ne bayan koken wasu daga cikin mahajjatan Najeriya suka yi, a yayin aikin hajjin na bana.
Sannan hukumar ta ce idan har kudin suka iso hannunsu, za su miƙa kudin hukumar jin dadin alhazan jihohi don ganowa da rarraba kudin abincin ga wadan lamarin ya shafa.