Ma’aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da cewa hare-hare ta sama da jiragen Amurka marasa matuka suka kai a Pakistan a watan da ya wuce ya hallaka jagoran kungiyar IS a Afghanistan.
Shi dai Hafiz Sa’eed Khan ya jagoranci kai hare-hare daban-daban da suka hallaka mutane da dama a cikin Afghanistan, kuma ko a baya an yi ta yada jita-jitar mutuwarsa.
A baya an yi ta rade-radin mutuwarsa, amma yanzu Amurka ta tabbatar an hallakashi a hare-haren hadin gwiwa da ake kaiwa tsakanin ta da sojojin Afghanistan. Shi dai Sa’eed Khan daya ne daga cikin shugabannin Taliban da ya hade kai da kungiyar IS.
A watan mayun shekarar nan ne hare-hare ta sama da Amurka ta kai a Pakistan suka hallaka shugaban kungiyar Taliban Mullah Akhtar Muhammad Mansour.