An hallaka mayakan boko haram da dama a arewacin Kamaru


 

 

Majiyar tsaron kasar Kamaru ta sanar da cewa Sojojin kasar sun hallaka mayakan boko haram da dama a arewacin kasar

Kafar watsa labaran Afirka time ta nakalto majiyar tsaron kasar Kamaru na cewa a safiyar jiya Alkhamis Sojojin kasar sun kai wani farmaki kan mayakan kungiyar boko haram a yankin Sandawadjirin na arewacin kasar tare da hallaka sama da  mayakan kungiyar boko haram 20 da kuma jikkata wasu da dama na daban.

Majiyar ta ce a ‘yan kwanakin nan kungiyar ta boko haram na shirye-shiryen kai hari kan sansanin Sojojin kasar domin haka Sojoji suna cikin shirin ko ta kwana na dakile duk wani ta’addanci da kungiyar ta boko haram ke shirin kaiwa cikin kasar.

A ranar Litinin din da ta gabata wata nakiya ta tashi da motar Sojoji a kan hanyar Wambaché zuwa Limani dake arewacin kasar, lamarin da ya yi mutuwar Sojoji guda uku.

Tun a shekarar 2009 ne kungiyar ta boko haram ta fara kai hare-haren ta a Najeriya, a shekarar 2015 din da ta gabata kungiyar ta fadada kai hare-haren zuwa kasashen Nijer, Chadi da kamaru.

You may also like